Posts

MUTUM DA HANKALI

Image
Mutane da Hankali 01 Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaba, Ja gaba, tare Ahalinsa da Sahabbansa.  Hankali shi ne mafi girman abin da Allah ya bawa ɗan Adam, ba wai don bai bawa sauran halittu shi ba, sai don yanda ɗan Adam yake amfani da hankalin na sa ya sha bambam da yanda sauran halittu suke amfani da na su hankalin. Hakan kuma ya samo asali ne saboda shi tunanin ɗan Adam yana samun jagoranci ne daga shari'a wadda Allah ya aiko manzanni da ita, don haka sai ɗan Adam ya zamana yayi fintinkau a ɓangaren kowace ɗabi'a mutuƙar.  Wani zai ce ai tun kafin a saukar da Shari'a mutum ya ke da hankali, sai mu ce, Allah da ya halicci Annabi Adam, ya halicceshi ne akan fiɗira, kuma haka aka ɗorawa Annabi Adam nauyin ɗora ƴaƴansa akan wannan tafarki wanda aka ɗorashi a kai.  Allah Mai Girma da Ɗaukaka ya na cewa: كَانَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً فَبَعَثَ اللَّهُ النَّبِيِّينَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ الْ...

ƘARYA

Image
ƘARYA. DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA ANNABIN RAHAMA SHUGABA JA GABA DA AHALINSA TARE DA SAHABBANSA DA WAYANDA SUKA BIYO BAYANSU DA KYAUTATAWA. NA SHAIDA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH KUMA ANNABI MUHAMMAD BAWANSA MANZONSA NE.  HAKIKA MAFI GASKIYAR ZANCE SHINE LITTAFIN ALLAH, KUMA MAFI ALHERIN SHIRIYA ITACE SHIRIYAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W), MAFI SHARRIN AL'AMURA KUWA SUNE WAYANDA AKA FARAR, KUMA DUKKANIN FARARREN ABU BIDI'A NE, KUMA DUKKANIN BIDI'A ƁATA CE. BAYAN HAKA, WANNAN WANI TAƘAITACCEN RUBUTU NE DA NAKE SO IN BIJIROWA YAN UWA SHI DON TUNATARWA DA KUMA FAƊAKARWA AKAN WANI MUHIMMIN ABU MAI GIRMA WANDA SABO DA SHI YA SANYA DA YAWANMU MUN DAINA GANIN GIRMANSA. BA WANI ABU BANE WANNAN FACE ƘARYA.  INA ROƘON ALLAH DA YA SANYA WANNAN AIKI YA ZAMO DON SHI AKAYI, YA KUMA KARƁI AIKIN, HAƘIƘA SHI MAI IKO NE MAI KUMA KARAMCHI NE. ƘARYA Ƙarya dai sananniyar aba ce, domin kuwa koda yaushe tana kaikawo a cikin mutane,...

LALLAI AKWAI TAMBAYA DANGANE DA NI'IMOMIN RAYUWA

“Sa'annan kuma haƙiƙa lallai sai an tambayeku game da ni'imomi.”  Duk wata ni'ima ta shiga cikin wannan, don haka idan Allah ya yiwa bawa wata ni'ima to tabbas ya shirya amsa tambayoyi ranar alƙiyama akan wannan ni'imar. Cikin hadisi ingantacce riwayar muslim, Annabi Muhammad (S.A.W) da manyan sahabbansa da kuma mafi kusancin abokanansa (Abubakar da Umar) (R.A) yunwa ta fito da su, a ƙarshe suka samu abinci a gidan ɗaya daga cikin sahabbai mawadata, suka ci suka ƙoshi kuma Annabi ya basu tabbacin cewa sai an tambayesu dangane da wannan ni'imar. Idan har abincin da ba kai ka nemo da guminka ba za'a tambayeka to ni'imomin da akai maka na lafiya da ƙwarewa a wani fanni na rayuwa sune mafi aula da'a tambaya. Idan kanada ƙarfin tunani da hangen nesa to tabbas za'a tambaye ka akan wannan ni'imar. Idan kana da fasahar tsara rubutu to tabbas za'a tambaye ka akan hakan. Idan kana da balagar magana, ka iya yin magana wadda za'a fahimta kuma ka ...

PROPHET MUHAMMAD (S.A.W) (AS AND IN... Series. 01)

PROPHET IN HIS HOME. In the name of Allah! Allah the exalted said “Certainly you have in the Messenger of Allah an excellent exemplar for him who hopes in Allah and the latter day and remembers Allah much.” (Qur'an Surat Ahzab  verse 21) If you want and hope to meet Allah and the day of judgement safely, you must follow the teachings and life lessons from the life of the prophet Muhammad (S.A.W). So you need to know how the messenger of Allah treated people around him... As a father, as a friend, as a teacher, as a leader, as a husband and so many more... Let the story of a prophet and his interaction with different kinds of people take most of your time; this will give you hardly any chance to study the life of celebrities, reading useless screeds was not even mentioned, much less watching time-burner movies... PROPHET AS A HUSBAND. Anas ibn Malik (R.A) related that he had not seen a man who was clement and nicer to his household members than the Apostle of Allah. The hadith is sa...

ALFAWA'ID 1

ALFAWA'ID   Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su tabbata ga zaɓaɓɓe fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).  Wannan wasu taƙaitattun bayanai ne ko kuma tunatarwa da na tsarasu don ƙaruwarmu baki ɗaya. Allah subhanahu wata'ala ya sanyamu mu amfani da abinda zamu karanta, ya kuma yafe mana kura-kuren da suke ciki. Kamar sauran rubuce-rubucen mu, wannan ma muna bada damar za'a iya yaɗawa yan'uwa domin shi aikin umarni da hani yana kan kowa da kowa. Allah nake roƙo daya sanya mu cikin bayinsa tsarkaka ma'abota Aljanna maɗaukakiya. Kuma shi nake roƙo daya karɓi wannan aiki namu. Haƙika shi mai karamchi ne mai kuma afuwa. SAƁANIN AL'UMMA Wasu matasa biyu sunyi sabani, har ta kaisu ga tada jijiyar wuya...  Sai wani dattijo yazo ya riskesu, ya tambaya ko akan me suke tada jijiyar wuya. Saina farkonsu yace, ce masa nayi mutanen duniya dukansu batattu ne, shiryayye shine wanda yabi shiriyar Allah da manzonSa (S.A.W)." Na biyun kuma sai y...

TARKON SHAIDAN

Tarkon Shaidan 1 SHIMFIDA Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su tabbata ga shugaba jagaba (S.A.W), da ɗalibansa kuma abokanan rayuwarsa (Sahabbai) da kuma mafiya tsarkin iyali a doron ƙasa (Ahlul baiti). Bayan haka.  Lokacin da ubangiji (S.W.A) ya halicci Annabi Adam (A.S) tare da Nana Hauwa'u kuma ya sanyasu a cikin Aljanna da Shaiɗan ya so ɓatar da su, bai zo musu kai tsaye da sunan mai ɓatarwa ba, hasalima ce musu yayi "Haƙiƙa ni a gareku mai yin nasiha ne..." bayan haka har rantsuwa ya yi musu ya kuma ƙawata umarninsa da wasu abubuwa da suke so (son mulki da son dawwama) duk don ya ɓatar da su... Kuma ya samu nasara. Mu tuna lokacin Annabi Nuhu da mutanensa, tabbas Shaiɗan bai ɓatar da su ba sai da ya yi amfani da tarkonsa ta hanyar nuna musu cewa lallai su a kan gaskiya suke kuma shi wanda aka turo ɗin ba shi da girman da za a turo shi zuwa garesu. Duba Annabi Yunus, shi ma Shaiɗan bai hanashi yaɗa da'awarsa ba, amma sai ya ɗana masa tarkon fu...