Posts

TABARBAREWAR ILMIN ZAMANI... INA MAFITA?

Ga wanda yake rayuwa cikin mutane, kuma yake cudanyuwa da yan makaranta, kuma yake zantawa dasu akan yanda karatukansu suke gudana, nasan ba zai jayayya ba idan nace tabbas ilmin zamani da hanyoyin samunsa suna cikin tsaka mai wuya. Musamman a arewacin Nigeria. Makarantu nawa ne suke gudanuwa ba tare da malamai ba...? Wata sananniyar makarantar gwabnati kwanaki haka dalibanta yan SS1 suka zo min, lokacin suna gab da barin ajin, suka sanar dani cewa basu da malamin biology tun farkon shigarsu SS1. Suka ce dani da can wani dan bautar kasa ne yake koyar dasu, tunda ya tafi kuwa basu da wani tsayayyen malami. Yaran sune wayanda ake tunanin sune masu son karatu a ajin. Amma idan kaji basic abubuwa na biology da basu sani ba sai abin ya daure maka kai. Abin mamakin shine su wayannan yaran ba zasu iya gina maka jimloli masu kyau na turanchi ba, ballantana azo maganar biology, physics, chemistry ko uwa uba mathematics.  Ka gaya min don me zamu ji mamakin idan yaran nan sun kasa cin jarraba...

HUKUNCIN ZAMAN HADE HANNU DA GWIWA YAYIN DA LIMAN YAKE HUDUBA.

Image
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Hadisi yazo daga Mu'adh bn Anas, wanda imam Ahmad ya rawaitoshi da kuma Imam Tirmidhi (514) cewa "Annabi ya hana zaman Ihtiba'i (zaman hade gwiwa da hannu kamar yadda yake a hoton sama) yayinda liman yake huduba." Zaman ihtiba'i shi ne mutum ya haÉ—e Æ™aurinsa da cinyarsa a zaune sannan ya kewaye su da hannayensa.  Wannan hadisi Imam Albaniy da wasu daga masu tahÆ™iÆ™in musnad sun ingantashi. Imam Nawawiy kuma da Ibnul Arabi sun da'ifanta hadisin tare da wasu malamai. (Tahzeeb Attahzeeb 4/258) Sai dai an samu cewa wasu daga cikin sahabbai sun yi irin wannan zama, yayin da liman yake tsaka da huÉ—uba, cikinsu akwai Abdullahi Bn Umar da Anas Bn Malik Allah ya Æ™ara yarda da su. Ibn Qudama cikin littafin Mugniy na sa, ya nuna babu laifi idan anyi wannan zama, harma ya nuna wannan itace fahimtar Ibn Musayyib, Hasanul Basariy, Ibn Sirin, Imam Malik da kuma Shafi'i da sauransu. Allah yayi musu rahama baki É—aya. Ibn Qud...

IDAN 'BERA DA SATA...

Da sunan Allah mai jin kai.  Duk lokacin da akace tarbiyya to ana maganar rayuwa ne baki daya, domin tarbiyya ke kawo kwanciyar hankali, zaman lafiya, albarka da abubuwa da dama na morewa zaman duniya. Mutane nawa ne suke da dukiya amma babu kwanciyar hankali ba kuma sa jin dadin dukiyar domin rashin aminchi da fargaba sun dabaibayesu?  Idan ka fahimchi wannan saika gane me muke nufi da morewa zaman duniya.  Idan muka karkato da tunaninmu zuwa ga rayuwar yara masu tasowa tabbas duk mai kula hankalinsa zai tashi. Bari mu kasa yaran gida uku don bayanin yafi fitowa fili. Kashi na farko, sune yaran da suke da gata kuma iyayensu suke kokari wajen basu kyakkyawan ilmi na zamani. Zaka iske irin wayannan yara suna tasowa da tsananin tsabagen rashin tarbiyya da wani tunani na babu wanda ya isa ya ja dasu ko kuma kaga suna jin cewa babu wanda ya isa ya taka su.... To ai sunada kudi sunsan indai a wannan kasar ne indai kanada kudi to sai yanda kayi da hukuma. Irin wayannan yara zak...

LIFE LESSONS FROM CELL BIOLOGY

Image
As zoology students, we learn many life lessons from cell biology, particularly in the chemical reactions that take place within a cell. It is not only the biological activity or chemistry of life that we learn. The cell, being the tiniest structure, offers many lessons, including leadership, unity, security, division of labour, and many more. The cell is a structural and functional unit of life in which all chemical reactions in our body take place. With these reactions and functions of the cell, humans have created transportation machines, robotic machines, and many electronic machines. Do you understand that the series of films you are watching is all the output of the cell? If we follow the lessons from cell biology, we will live our lives the way Almighty Allah wants us to. So to say; In everything, there is a sign indicating that Allah is one. Without wasting our time, which is always ticking (clocking), let us move directly to some lessons. Let us take the nucleus, which is like...

WAIWAYE ADON TAFIYA (41-45)

WAIWAYE ADON TAFIYA (41) Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W)... Kuraishawa sun san sun tafka kuskure, don haka suka rasa zaune suka rasa tsaye, a karshe sai suka yanke cewar gwara su aika wani daga cikinsu don yaje ya sabunta yarjejeniya da Annabi Muhammad (S.A.W) ta sulhun Hudaibiyya.  Ai kuwa saiya dauki hanya ya nufo madina, haka ya wanzu yana tafiya har ya sadu da  madina, da zuwansa saiya zarce gidan yarsa wadda take matar Annabi Muhammad (S.A.W) Ummu Habiba.   Bayan ya shiga wajenta ga gajiyar hanya sai yayi yunkurin zama ya akan gadonta amma bisa ga mamakinsa saita hanashi zama akan wannan gado tace mishi bazai zauna ba domin shi ba mai tsarki bane. Ya cika da mamaki, yau ga yarsa tana daukaka darajar wani mutum sama da tasa... Daga nan saiya nufaci wajen Annabi Muhammad (S.A.W), a zuciyarsa yana tuno irin rashin kyautawar da suka yiwa Annabi tun daga farkon fara da'awarsa zuwa yanzu. Ya tuno irin kisan gillar da suka rinka yiwa sahabbai, da kuma irin cutarwar da...

living in Bubble?

Are we really living in a bubble? No matter how great the discovery, no matter how long it takes to consume, nor matter how many professors contribute... We count it as zero if it's incompatible with the Holy Qur'an.  We believed Qur'an and modern science are compatible. What is a science without religion?  It's not a matter of living in a bubble... To live in a bubble means rejecting new changes or knowledge completely... Muslims are always ready to accept new good knowledge and new discoveries, and they are not debunking any discovery unless it contradicts the holy Qur'an.  For the safety of your imaan learn Qur'an first. It will guide, protect and save you from traps. "I did not understand", said one of the immature atheists. "How can you understand," I said  "you who see with only two eyes. Go and learn the two knowledge deeply from the root..." I completed I miss Safiyya Usman from Facebook. May Allah guide her if she is alive....

Knowledge Givers

Givers never lack! I discovered that, those that normalize teaching, they are far better than those normalize reading. And a person who normalize the former and the latter is better.   Thats amongst the secrets behind the saying of Prophet Muhammad (S.A.W) to his beloved Companions (R.A) "Convey from me even one verse..." May Almighty guide us to the right path. Naseeb Auwal Abu Umar Alkanawy.