Posts

WAIWAYE ADON TAFIYA (36-40)

WAIWAYE ADON TAFIYA (36)  Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W) A dai wannan yaki da akai a banu musdalik wani babban al'amari ya faru. Kamar yadda muka nuna a rubutun daya gabata cewa ba'a samu yakin da kafirai suka fita da yawa ba irin wannan yaki. Ba don komai ba sai don kudirinsu na ganin sun tarwatsa musulunchi sun shiga tsakanin Annabi da sahabbansa, sun kunna wutar adawa tsakanin sashen sahabbai. Har ma suna ganin idan sun samu dama don zubar da mutunchin Annabi zasu kulla kullalliya don yin wani abu wanda zai zamo aibu a cikin gidansa. Saidai Allah bai basu iko ba. Nana Aisha da kanta take bamu labari. Cikin hadisi ingantacce wanda Bukhari da Muslim suka fitar dashi. Zamu kawo a takaice. Kamar yadda muka sani idan Annabi zaiyi tafiya yakanyi kuri'a a tsakanin matansa, wadda ta fada kanta to da ita za'a fita. A wannan lokaci sai akayi sa'a sunan Nana Aisha ya fito. Sai Nana Aisha ta shirya aka tafi. A wannan lokaci kuwa an saukar da ayar hijabi. Wani dan daki ...

WAIWAYE ADON TAFIYA (31 - 35)

WAIWAYE ADON TAFIYA (31) Tatacciyar Sirad Ma'aiki (S.A.W) Safiya bnt Abdulmuddalib yar uwar Hamza ibn Abdulmuddalib ce,   labari kuma ya riga ya risketa cewa an kashe dan'uwa don haka ta taso don ganin gawar dan'uwanta shugaban shahidai Hamza (R.A). Annabi baya son taga gawar don kada hankalinta ya tashi saboda irin kisan da akaiwa dan'uwanta, don haka saiya umarci danta Zubair Bn Awwam daya hanata karasowa inda gawar Hamza take. Dan nata yayi maza ya tare ta ya gaya mata cewa Annabi  baya son taje don ganin wannan gawa. Budar bakinta ke da wuya sai tace "Saboda me? Ai nasan an yiwa dan'uwana kisan wulakanci, sai dai akan tafarkin Allah ne kuma ina burin Allah zai saka masa da mafificin alheri, ni kuma insha Allah zan zama mai hakuri." Daga nan taje taga Hamza tayi masa addu'a. Bayan nan Annabi yasa aka binneshi anan filin Uhud kabarinsa har yau yananan.  Mus'ab wanda ya daukarwa musulmi tuta a wannan yaki na Uhudu, ya kasance mafi kwalliyar mutane...

WAIWAYE ADON TAFIYA (26 - 30)

WAIWAYE ADON TAFIYA (26) Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W) Yanayin yanda sahabbai suka ga Annabi ya basu umarni, da kuma yadda suka ga bai damu da cewa da yawansu su fita ba sai sukayi tsammanin ba yaki za'a gwabza ba. Don haka adadin musulman yayi karanchi sosai. Domin kuwa wayanda suke da dabbobi amma a nesa Annabi bai basu umarni suje su dauko ba, hasalima da sukai niyyar su dauko dakatar dasu yayi bai kuma tsaya jiransu ba yayi gaba tare da sauran sahabbai.  A karshe Annabi ya fita da sahabbai adadin Dari uku da goma sha uku (313). Cikinsu mutum dari biyu da arba'in da yan kai duka mutanen madina ne, wato Ansarawa, ragowar kuwa mutanen Makkah ne ma'abota hijira wato muhajirai.   (Nurul Yakeen 89) Kasancewar Abu sufyan masanin hanya, bayan ya turawa kafiran Makkah abinda ke gab da faruwa na tare ayarinsu da za'ai, saiya sauya hanya, kuma cikin sa'a sai ya kewaye wa su Annabi. Ganin ya tsira saiya tura da sako zuwa ga kafiran Makkah yana umartarsu dasu koma tun...