Kwarafshan
Kwarafshan! Menene kwarafshan? Kwarafshan shine lokacin da wannan yarinyar take bawa iyayenta kudi saboda suyi gum da bakinsu su zuba mata ido ta kula kowane kowane banza. Kwarafshan shine wannan saurayin da zaije yayita yiwa budurwa karyar kudi kawai don cinwa wata manufa tasa ta banza. Kwarafshan shine lokaci da kace "eh" sukace "a'a". Suka biyaka kudi don kace " a'a", kuma ka karba kabi hanyarsu ta banza. Kwarafshan shine lokacin da shugaban kasar nan ya bada sunan wani a matsayin minista, su kuma yan majalisa suka nemi wanda aka bada sunan nasa daya basu kudi indai yana so su tabbatar dashi... Shikuma saboda son abin duniya ya basu kudin shima ya zama mutumin banza. Kwarafshan shine lokacin da wannan Dan sanda ya karbi kudi a hannun mai laifi kuma ya sakeshi. Kwarafshan shine lokacin da dalibai suka biya wannan malamin kudi don jarrabawarsu tayi kyau. Kwarafshan shine lokacin da aka baka kudi ranar zabe kuma ka zabi mutumin da bai chanchanta b...