MUHIMMANCIN ADDU'A A RANAKUN JUMA'A DA LARABA.
INGANCIN AMSA ADDU'A RANAR JUMA'A KO RANAR LARABA. Dangane da ranar Juma'a hadisai ingantattu sun tabbata waƴanda kai tsaye Annabi Muhammad ya faɗi cewa a a ranar juma'a akwai wata sa'a da mutum idan yayi addu'a babu makawa sai an amsa masa. Akwai ruwayar Abu Huraira (R.A) cikin Sahihul Bukhari (935) da Sahihu Muslim (852), da kuma ruwayar Abdullahi Ibn Salam (R.A) cikin Ibn Sunan Majah (1138) da Musnad Imam Ahmad (23458). Cikin wannan ruwayoyin biyu hadisan sun nuna duk wanda ya kasance yana sallah a wannan sa'ar kuma yayi addu'a to babu makawa za a amsa masa wannan addu'ar. Akwai kuma ruwayar Jabir Ibn Abdullahi (R.A) a Sunan Abi Dawud (1046), Sunan Nasa'i (1389) da kuma Sunan Ibn Majah (1139). Wanda shi kuma a tasa ruwayar ya nuna cewa lokacin shi ne bayan sallar La'asar, sannan bai ambaci cewa sai mutum yana sallah ba. Mafi yawan malamai sun tafi akan cewa lokacin amsa addu'a a Ranar Juma'a shi ne bayan Sallar La...