Posts

ALFAWA'ID 1

ALFAWA'ID   Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su tabbata ga zaɓaɓɓe fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).  Wannan wasu taƙaitattun bayanai ne ko kuma tunatarwa da na tsarasu don ƙaruwarmu baki ɗaya. Allah subhanahu wata'ala ya sanyamu mu amfani da abinda zamu karanta, ya kuma yafe mana kura-kuren da suke ciki. Kamar sauran rubuce-rubucen mu, wannan ma muna bada damar za'a iya yaɗawa yan'uwa domin shi aikin umarni da hani yana kan kowa da kowa. Allah nake roƙo daya sanya mu cikin bayinsa tsarkaka ma'abota Aljanna maɗaukakiya. Kuma shi nake roƙo daya karɓi wannan aiki namu. Haƙika shi mai karamchi ne mai kuma afuwa. SAƁANIN AL'UMMA Wasu matasa biyu sunyi sabani, har ta kaisu ga tada jijiyar wuya...  Sai wani dattijo yazo ya riskesu, ya tambaya ko akan me suke tada jijiyar wuya. Saina farkonsu yace, ce masa nayi mutanen duniya dukansu batattu ne, shiryayye shine wanda yabi shiriyar Allah da manzonSa (S.A.W)." Na biyun kuma sai y...

TARKON SHAIDAN

Tarkon Shaidan 1 SHIMFIDA Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su tabbata ga shugaba jagaba (S.A.W), da ɗalibansa kuma abokanan rayuwarsa (Sahabbai) da kuma mafiya tsarkin iyali a doron ƙasa (Ahlul baiti). Bayan haka.  Lokacin da ubangiji (S.W.A) ya halicci Annabi Adam (A.S) tare da Nana Hauwa'u kuma ya sanyasu a cikin Aljanna da Shaiɗan ya so ɓatar da su, bai zo musu kai tsaye da sunan mai ɓatarwa ba, hasalima ce musu yayi "Haƙiƙa ni a gareku mai yin nasiha ne..." bayan haka har rantsuwa ya yi musu ya kuma ƙawata umarninsa da wasu abubuwa da suke so (son mulki da son dawwama) duk don ya ɓatar da su... Kuma ya samu nasara. Mu tuna lokacin Annabi Nuhu da mutanensa, tabbas Shaiɗan bai ɓatar da su ba sai da ya yi amfani da tarkonsa ta hanyar nuna musu cewa lallai su a kan gaskiya suke kuma shi wanda aka turo ɗin ba shi da girman da za a turo shi zuwa garesu. Duba Annabi Yunus, shi ma Shaiɗan bai hanashi yaɗa da'awarsa ba, amma sai ya ɗana masa tarkon fu...

HANYAR TSIRA

1 A Gida babu aminchi, a Makaranta babu aminchi, akan hanya babu aminchi, a kasuwa, a Asibiti, a Tasha, a gurin taro, a masallachi..... ko inama babu aminchi. Duhu mai girma ya baibaye ko'ina hatta cikin zukatan mafi yawan mutane yayi bakikkirin, jinin dake gudana daga zuciyarmu zuwa sassan jikinsu yayi bakikkirin........... ganin idonmu yayi rauni bama iya banbace abubuwa masu kamanceceniya da wayanda basu da kamanceceniya.......  Menene ya janyo hakan duka? Ko shakka babu son zuciya ne ya kawo haka. Da za'a zuba tsaron duka duniyar nan, amma ya zamana zukata basu gyaru ba, to tabbas babu aminchi. Da za'a halicci rana guda goma a sararin samaniya don su haske duniya, to da tabbas za'aci gaba da rayuwa cikin duhu domin kuwa hasken dake cikin zukata shine haske bawai hasken dake waje ba...... Tarbiyya ta lalace, zina ta yawaita, sata, neman maza/mata, karya duk sun mamaye al'umma.😭 Da kanmu mun bude kofar rashin aminchi da tashin hankali kuma mun afka cikin birnin S...

WAIWAYE ADON TAFIYA 46 - 50

WAIWAYE ADON TAFIYA (46 - 50) Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W) Annabi bai bar Da'if ba har saida yayi musu addu'ar shiriya. A wannan shekara ta takwas bayan Hijira aka haifawa Annabi santalelen yaro, Mariya ce ta haifeshi. Anas (R.A) wanda rainon Annabi ne yana bada labari cewa bayan an haifi Ibrahim (R.A), Annabi Muhammad ya fito ga sahabbai yake sanar dasu cewa, da daddare an haifa masa yaro kuma ya sanyawa yaron sunan Babansa Ibrahim (A.S).  Matan madina suka rinka tururuwa cewa suna son su shayar da wannan dan albarkar yaro suna masu neman albarka saboda mahaifiyar yaron tana da karanchin abinda zata shayar dashi. A karshe Annabi ya damka Ibrahim a hannun Ummu Saif. Wannan sahabin wanda ya samu tarbiyya a gidan manzon Allah wato Anas Bn Malik yake kara cewa bai taba ganin mutum mai so da jinkan iyalansa ba kamar manzon Allah, domin ya kasance yana yawaita shiga inda Ibrahim din yake ya daukeshi ya kuma sumbaceshi.  A shekara ta tara sai shugabanni suka rinka bijirowa su...