ZUNUBI YANA MUNANA ZUCIYA DA SIFFAR MUTUM.
ZUNUBI YANA MUNANA ZUCIYA DA HALITTAR MUTUM
Babu shakka, zunubi yana lalata zuciyar bawa, kuma idan zuciya ta lalace, tasirinta yana bayyana a rayuwar mutum, a halayensa, har ma da kamanninsa. Wannan shi ya sa duk wanda yake son kyakkyawar rayuwa da annurin fuska, to ya yawaita biyayya ga Allah, ya nisanci saɓo.
Kyawun halitta ba shi ne abin da Allah yake dubawa ba, domin kuwa Allah ba ya duba izuwa surar mutum ko dukiyarsa, shi yana duban zuciya ne da kuma ayyuka. Idan kana aiki nagari to da sannu zuciya za tai haske, kuma hasken zai bayyana a siffarka tare da kwarjini, annuri da farin jini da kuma kwarin jiki, kamar yanda idan zunubai suka taru suke mayar da zuciyar baƙa wuluk ta yanda bakin zai gadar maka da ciwukan zuciya, irinsu hassada, ƙyashi da baƙin ciki, sannan zai cire annurin daga fuskarka, wofantar da kai a zuƙatan bayi.
Allah Maɗaukakin yana cewa:
> {}كَلَّا بَلْ ۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ{}
"A'aha! Abin da suka kasance suna aikatawa ne ya lullube zukatansu."
(Suratul Muṭaffifīn: 14)
Wannan aya tana nuna cewa zunubai suna barin baƙin tabo a zuciya har su rufe ta daga karɓar gaskiya.
Kuma Annabin Allah ﷺ ya fassara wannan a cikin hadisi ingantacce in da ya ke cewa:
"Lallai idan bawa ya aikata zunubi, ana sanya baƙin ɗigo a zuciyarsa. Idan ya tuba ya nemi gafara, zuciyarsa sai ta tsarkaka. Idan ya ci gaba da aikata zunubi, sai baƙin ya ƙaru har ya rufe zuciyarsa. Wannan shi ne 'Ar-Raan' da Allah Ya ambata."
(Tirmidhi: 3334, Ibn Majah: 4244. Albani ya inganta shi.)
Haka kuma ya tabbata daga Annabi ﷺ cewa:
"Hajarul Aswad ya sauko daga Aljanna yana da fari fiye da madara, sai zunuban ƴan Adam suka mayar da shi baƙi."
(Ahmad, Tirmidhi. Albani ya inganta shi a As-Silsilah As-Saḥīḥah lamba ta 2390.)
A wata riwaya kuma:
"...zunuban mushrikai ne suka mayar da shi baƙi."
(Ibn Khuzaimah)
Idan har dutse wanda ya fito daga Aljanna ya canza launi saboda tasirin zunuban mutane, to zuciyar ɗan Adam da jikinsa sun fi cancantar su sami tasirin zunubi.
Abdullahi bn Abbas (R.A) ya ce:
"Lallai kyakkyawan aiki yana haifar da haske a fuska, annuri a zuciya, yalwa a arziki, ƙarfi a jiki da soyayya a zukatan mutane. Zunubi kuwa yana haifar da baƙi a fuska, duhu a zuciya, rauni a jiki, ƙarancin arziki da ƙiyayya a zukatan mutane."
Shaikhul-Islam Ibn Taymiyyah (R) ya tabbatar da wannan ma'ana, a gurare da dama a littafansa, a cikin shahararren littafin nan nasa Al'istiqama yana cewa:
"Ayyukan alheri suna da haske a zuciya, da annuri a fuska, da samar da ƙarfi a jiki da kuma sanya soyayya a zuƙatan mutane. Munanan ayyuka kuwa suna da duhu a zuciya, da baƙi a fuska, da samar da rauni a jiki da sanya ƙiyayya a zuƙatan mutane."
Dalibinsa, Al-Imam Ibnul Qayyim (R) shi ma a mabanbanta gurare a littafansa yana nuni da cewa:
Daga cikin hukuncin zunubi akwai cewa yana kashe hasken zuciya. Idan hasken zuciya ya mutu, duhu yana bayyana a fuska da gaɓoɓi.
(Al-Jawabul Kafi.)
A cikin Ighathatul Lahfan ya ƙara da cewa "Biyayya tana samar da haske a fuska, annuri a zuciya, yalwar arziki da soyayya a zuƙatan halitta. Zunubi kuma yana da baƙi a fuska, duhu a zuciya, ƙunci a rayuwa da ƙiyayya a zuƙatan halitta."
Saboda haka, komai rashin kyawun halittar mutum, idan ya kyautata alaƙarsa da Allah, Allah zai ba shi annuri da kwarjini, kuma Ya sanya masa karɓuwa a zukatan bayinsa. Haka kuma, yawaita zunubi yana rage wa mutum wannan annuri da karɓuwa, musamman a wurin masu imani.
Idan kuma ka ga ana son wani mai bayyana da zunubai, kada ka ɗauka cewa wannan alama ce ta yardar Allah. Domin wani lokaci hakan jarrabawa ce ko kuma istidrāj (talala) ne. Don haka, idan mutum ya ji zuciyarsa tana karkata ga son masu yaɗa fasadi da alfahari da saɓon Allah, ya binciki zuciyarsa, ya yawaita tuba da istigfari, domin zuciya mai rai tana ƙin saɓon Allah, ko da tana tausayin mai zunubi.
Shaidan haka yake ƙawata wa mutane munanan ayyuka har su riƙa ganin su a matsayin kyawawa. Kamar yanda Allah ya ke cewa:
{}أَفَمَن زُيِّنَ لَهُ سُوءُ عَمَلِهِ فَرَآهُ حَسَنًا{}
"Shin wanda aka ƙawata masa munin aikinsa har ya gan shi mai kyau..." (Fāṭir: 8)
Shi ya sa wasu suke alfahari da shaye-shaye, wasu da zina, wasu da liwaɗi, wasu kuma da sauran nau'ikan saɓon Allah, suna ganin wannan shi ne wayewa da ci gaba. Alhali kuwa wannan yana daga cikin sakamakon nisantar Allah da lalacewar zuciya.
Shi yasa musulunci ya zo mana da addu'o'i kala-kala na wanke zuciya da tabbatar da imani a cikinta, da sanyayata daga zafin zunubai ta hanyar wanketa kamar yanda ake wanke farin tufafi da kuma sanyayata da ƙanƙara, domin zunubai suna gadarwa zuciyar wani zafi da ɗumi.
Allah Ya tsare mu daga zunuban da suke kashe zuciya, su ɗauke annurin fuska, su hana karɓuwa a duniya da Lahira.
✍️ Abu Umar Alkanawy
Comments
Post a Comment