ƘARYA

ƘARYA. DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA ANNABIN RAHAMA SHUGABA JA GABA DA AHALINSA TARE DA SAHABBANSA DA WAYANDA SUKA BIYO BAYANSU DA KYAUTATAWA. NA SHAIDA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH KUMA ANNABI MUHAMMAD BAWANSA MANZONSA NE. HAKIKA MAFI GASKIYAR ZANCE SHINE LITTAFIN ALLAH, KUMA MAFI ALHERIN SHIRIYA ITACE SHIRIYAR ANNABI MUHAMMAD (S.A.W), MAFI SHARRIN AL'AMURA KUWA SUNE WAYANDA AKA FARAR, KUMA DUKKANIN FARARREN ABU BIDI'A NE, KUMA DUKKANIN BIDI'A ƁATA CE. BAYAN HAKA, WANNAN WANI TAƘAITACCEN RUBUTU NE DA NAKE SO IN BIJIROWA YAN UWA SHI DON TUNATARWA DA KUMA FAƊAKARWA AKAN WANI MUHIMMIN ABU MAI GIRMA WANDA SABO DA SHI YA SANYA DA YAWANMU MUN DAINA GANIN GIRMANSA. BA WANI ABU BANE WANNAN FACE ƘARYA. INA ROƘON ALLAH DA YA SANYA WANNAN AIKI YA ZAMO DON SHI AKAYI, YA KUMA KARƁI AIKIN, HAƘIƘA SHI MAI IKO NE MAI KUMA KARAMCHI NE. ƘARYA Ƙarya dai sananniyar aba ce, domin kuwa koda yaushe tana kaikawo a cikin mutane,...