HANYAR TSIRA
1 A Gida babu aminchi, a Makaranta babu aminchi, akan hanya babu aminchi, a kasuwa, a Asibiti, a Tasha, a gurin taro, a masallachi..... ko inama babu aminchi. Duhu mai girma ya baibaye ko'ina hatta cikin zukatan mafi yawan mutane yayi bakikkirin, jinin dake gudana daga zuciyarmu zuwa sassan jikinsu yayi bakikkirin........... ganin idonmu yayi rauni bama iya banbace abubuwa masu kamanceceniya da wayanda basu da kamanceceniya....... Menene ya janyo hakan duka? Ko shakka babu son zuciya ne ya kawo haka. Da za'a zuba tsaron duka duniyar nan, amma ya zamana zukata basu gyaru ba, to tabbas babu aminchi. Da za'a halicci rana guda goma a sararin samaniya don su haske duniya, to da tabbas za'aci gaba da rayuwa cikin duhu domin kuwa hasken dake cikin zukata shine haske bawai hasken dake waje ba...... Tarbiyya ta lalace, zina ta yawaita, sata, neman maza/mata, karya duk sun mamaye al'umma.😠Da kanmu mun bude kofar rashin aminchi da tashin hankali kuma mun afka cikin birnin S...