TABARBAREWAR ILMIN ZAMANI... INA MAFITA?
Ga wanda yake rayuwa cikin mutane, kuma yake cudanyuwa da yan makaranta, kuma yake zantawa dasu akan yanda karatukansu suke gudana, nasan ba zai jayayya ba idan nace tabbas ilmin zamani da hanyoyin samunsa suna cikin tsaka mai wuya. Musamman a arewacin Nigeria. Makarantu nawa ne suke gudanuwa ba tare da malamai ba...? Wata sananniyar makarantar gwabnati kwanaki haka dalibanta yan SS1 suka zo min, lokacin suna gab da barin ajin, suka sanar dani cewa basu da malamin biology tun farkon shigarsu SS1. Suka ce dani da can wani dan bautar kasa ne yake koyar dasu, tunda ya tafi kuwa basu da wani tsayayyen malami. Yaran sune wayanda ake tunanin sune masu son karatu a ajin. Amma idan kaji basic abubuwa na biology da basu sani ba sai abin ya daure maka kai. Abin mamakin shine su wayannan yaran ba zasu iya gina maka jimloli masu kyau na turanchi ba, ballantana azo maganar biology, physics, chemistry ko uwa uba mathematics. Ka gaya min don me zamu ji mamakin idan yaran nan sun kasa cin jarraba...