WAIWAYE ADON TAFIYA (36-40)
WAIWAYE ADON TAFIYA (36) Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W) A dai wannan yaki da akai a banu musdalik wani babban al'amari ya faru. Kamar yadda muka nuna a rubutun daya gabata cewa ba'a samu yakin da kafirai suka fita da yawa ba irin wannan yaki. Ba don komai ba sai don kudirinsu na ganin sun tarwatsa musulunchi sun shiga tsakanin Annabi da sahabbansa, sun kunna wutar adawa tsakanin sashen sahabbai. Har ma suna ganin idan sun samu dama don zubar da mutunchin Annabi zasu kulla kullalliya don yin wani abu wanda zai zamo aibu a cikin gidansa. Saidai Allah bai basu iko ba. Nana Aisha da kanta take bamu labari. Cikin hadisi ingantacce wanda Bukhari da Muslim suka fitar dashi. Zamu kawo a takaice. Kamar yadda muka sani idan Annabi zaiyi tafiya yakanyi kuri'a a tsakanin matansa, wadda ta fada kanta to da ita za'a fita. A wannan lokaci sai akayi sa'a sunan Nana Aisha ya fito. Sai Nana Aisha ta shirya aka tafi. A wannan lokaci kuwa an saukar da ayar hijabi. Wani dan daki ...