WAIWAYE ADON TAFIYA (26 - 30)
WAIWAYE ADON TAFIYA (26) Tatacciyar Sirar Ma'aiki (S.A.W) Yanayin yanda sahabbai suka ga Annabi ya basu umarni, da kuma yadda suka ga bai damu da cewa da yawansu su fita ba sai sukayi tsammanin ba yaki za'a gwabza ba. Don haka adadin musulman yayi karanchi sosai. Domin kuwa wayanda suke da dabbobi amma a nesa Annabi bai basu umarni suje su dauko ba, hasalima da sukai niyyar su dauko dakatar dasu yayi bai kuma tsaya jiransu ba yayi gaba tare da sauran sahabbai. A karshe Annabi ya fita da sahabbai adadin Dari uku da goma sha uku (313). Cikinsu mutum dari biyu da arba'in da yan kai duka mutanen madina ne, wato Ansarawa, ragowar kuwa mutanen Makkah ne ma'abota hijira wato muhajirai. (Nurul Yakeen 89) Kasancewar Abu sufyan masanin hanya, bayan ya turawa kafiran Makkah abinda ke gab da faruwa na tare ayarinsu da za'ai, saiya sauya hanya, kuma cikin sa'a sai ya kewaye wa su Annabi. Ganin ya tsira saiya tura da sako zuwa ga kafiran Makkah yana umartarsu dasu koma tun...