WAIWAYE ADON TAFIYA. (6 - 10)
WAIWAYE ADON TAFIYA 6 Tatacciyar sirar Ma'aiki (S.A.W)... Masoyi (S.A.W) tun daga yarintarsa ya taso da dabi'u mafi kyawu, dubi yadda muka bada labari yadda kwanakin jahiliyya suke, amma sai Allah ya bawa Annabi muhammad kariya daga dukkanin wasu halaye ababen kyamata. Da ace a yarintar Annabi an sameshi da wani laifi, kamar karya, rashin girmama na gaba, tsananin son mulki da sauran halaye to da abokan adawarsa sun tada jijiyoyin wuya akan abinda aka sameshi dashi mara kyau. Amma sai Allah ya tsarkakeshi tsarkakewa. Mafi girman abinda larabawa suka himmatu akai a wayannan kwanaki akwai caca, shan giya da kuma bautar gumaka, amma Annabi bai taba yin koda daya daga cikin wannan ba. Domin ya haramtawa kansa shan giya, caca, bautar gumaka ko kuma cin abin yankan da aka yankashi ga gunki. Tun a yarintarsa ya tsani gumaka kamar yadda ya tsani waka da alfasha... (Nurul Yaqeen 23) Har saida mutane suke kiransa da sunaye na girmamawa da karramawa, cikin wayannan sunaye akwai A...