Majalisar Mallam Jatau
0️⃣1️⃣ Sakamakon kowa yana zaman gida, hakan yasa majalisar kullum take cike da mutane tare da cewa ba wani yawan kirki ne dasu ba. Domin a unguwar akwai wayanda suka yarda dasu killace kawunansu kamar yadda gwabnati ta bukata, wasu kuma suna fita don yin harkokinsu. Amma shi mallam jatau da wasu tsirarun mutane sai suka zabi cewa zasu rinqa zaman majalisa da tattauna matsalolin rayuwa na yau da kullum. Ranar farko abinda aka fara tattaunawa shine matsalar gidan aure. Inda a karshe matsayar da suka samu shine; ana samun matsala bayan aurene saboda irin soyayyar da ake nunawa a waje kafin aure ba a nuna koda makamanciyarta a gidajen aure. Don haka sai mallam jatau yayi musu huduba a ciki yake cewa _Kamata yayi ku rinqa taya matanku ayyukan gida da rainon yara da girki........_ yayi musu bayani sosai suka gamsu. Bayan majalisa ta tashi. Mutum na farko ya koma gida, shigarsa keda wuya ya iske matarsa tana harhada kayan shan ruwa. Yana ganinta yayi murmushi yace “Zee baby” Ta dago cik...