ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU
ADON SALLAH A KASAR HAUSA A YAU. Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. 👉🏼Lokacin da akace musulmi ana nufin wani mutum wanda ya mika wuyansa ga Allah, ya hakura da son zuciyarsa, kuma ya zabi yayi rayuwa yadda musulunchi ya tsara masa. 👉🏼Idan akace Musulunchi, to wani addinine wanda bai bar komai ba saida yayi magana akansa, tun daga kan bautar Allah har zuwa shiga bandaki, cin abinci, kallon madubi, taje kai da kuma yanayin tsarin kwalliya. 👉🏼In kuwa hakane musulmi yana da kyau ya zama musulmi, kuma yana da kyau ya zama mai bin koyarwa addinin musulunchin. Bana mantawa da wani umarni da ubangiji ya bayar cewa _A shiga musulunchi gaba daya, kada abi hanyoyin shaidan_. Wato dukkanin tsarin rayuwa ya zama yadda Allah ya tsara bisa koyarwar sunnar masoyi (S.A.W) ba tare da an karkace anbi hanyar shaidanu ba. 👉🏼A watan azumi ana kokari mutuka wajen bauta, da kuma komawa ga Allah, saidai k...