SHARHIN HADISI NA 19
Daga Ibn Abbas Allah ya yarda da su yace "Wata rana na kasance a bayan Annabin rahama , sai yace da ni "Ya kai yaro, ka kiyaye (dokokin) Allah, zai kiyaye ka. Ka kiyaye (dokokin) Allah, za ka same shi a gabanka. Idan za kai roƙo, ka roƙi Allah. Idan za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah. Kuma ka sani, lallai da al'umma za su taru don su amfanar da kai da wani abu, ba za su amfanar da kai da komai ba, sai da abin da Allah ya rubuta a gareka. Kuma haka nan da za su taru don su cutar da kai da wani abu, ba za su iya cutar da kai ba, sai da abin da Allah ya rubuta a gareka. An ɗage alƙaluma, kuma takardun sun bushe... Wannan ruwayar Imam Tirmidhi ce, kuma sanadin ingantacce ne. Bayan Imam Tirmidhi Imam Ahmad ma ya fitar da shi, haka nan Imam Darimiy da Imam Dabaraniy a Mu'ujamul Kabir . Imam Tirmidhi ya ingantashi, haka nan Imam Nawawiy da Albaniy . Wannan hadisi ya tattare bayanai da fa'idoji da yawa wanda kowace fa'ida a ciki abar ayi rubutu mai zaman...