Posts

Showing posts from June, 2024

LIKITAN ZUCIYA...

Image
LIKITAN ZUCIYA....  BABI NA FARKO Me yake damuna? Anya kuwa ina da imani irin wanda mutanen kwarai suke da shi? Wayannan sune tambayoyin da suke kai kawo a cikin zuciyata. A wasu lokutan idan na roki Allah ina jin nauyi, domin ina tsananin neman tallafinsa, alhalin ni kuma bana sadar da abubuwan da ya umarceni da in sadar, hakanan bana nesantar da dama daga cikin abubuwan da yace in nesanta da su... Kunyar da nake ji tana ƙaruwa idan Allah ya biya min buƙatuna, duk da cewar ni bana aikata abubuwa da dama da yake so kuma ya yarda dasu... Gashi inayin iyaƙar ƙoƙarina domin kaucewa abin da Allah mai girma da ɗaukaka ya haramta, amma wani lokacin sai son zuciya yayi rinjaye a kaina in keta alfarma da girman Allah, in gudu inda nake ganin babu mai ganina, in saɓawa Allah wanda shi yana ganina a kowane lokaci, a kowane yanayi a kuma ko ina... tabbas malamai sun yi gaskiya da sukace wanda yafi karfin zuciyarsa, yafi wanda yake iya rusa birni shi kaɗai jarumta.. .  Wai menene yake