SHUGABANCHI 1
SHUGABANCHI .... Sabuwar hanya na bi , don wayar da kan al'umma akan halin da suke ciki a rayuwar yau . Na tsara bayanin nawa ta sigar labari ta yadda yan'uwa zasu karantashi cikin nishadi da kuma walwala . Ina fatan hakan bazaisa yan'uwa su kasa gane darussan da yake dauke da su ba . ** ** ** Farko Duk da iskar da take kadawa mai karfi hakan bai hana mutane fuskantar inda suka saka gaba ba. Mafi yawansu zaka iske cewa matasa ne kuma an zana kalmar FUSHI a fuskokinsu.... Suna tafe wasu basa ko magana yayinda zakaga wasu suna musayar magananganu a tsakaninsu.....